Bangaskiyar Jarumi - Jerin
Wahala domin sunan Kristi tana faruwa a duk fadin duniya kuma muna da alhakin yin addu'a da tallafawa 'yan'uwanmu maza da mata a cikin wadannan kasashe masu wahala. A cikin wadannan gajerun fina-finai guda takwas daga Muryar Shahidai, mabiyan Kristi wadanda aka tsananta musu a cikin nahiyoyi uku suna bada labarin bege da bangaskiyar su a cikin tsaninin wahala. Tsayyayar bangaskiya da yafewa da suka yi a gaban masu azabtarwa zai tunatar mana da manyan zukatan 'yan'uwanmu maza da mata na sauran duniya.